ICAN Taci Alwashin Warware Matsalolin  Kasuwanci A Kano – In Ji Sabon Shugabanta

FB IMG 1719815645588

Kungiyar kwarararun Akantoci ta kasa reshen jahar kano ta yi alwashin ba da gagarumar gudummawa wajen magance matsalolin harkokin kasuwanci.

Alfijir labarai ta ruwaito sabon shugaban kungiyar Alh. Sa’idu Isa Bala wanda aka zaba a karo na 43 ne bayyana haka a lokacin rantsar da sababbin shugabanin kungiyar a birnin kano.

Ya ce kungiyar ta lura rashin shigar da kwararrun Akantoci harkokin ‘yan kasuwa da masana’antu da kamfanoni yana haifar da nakasu matuka a harkokin kasuwanci.

Bala wanda ya bayyana kwararrun Akantoci  a matsayin maganin matsalolin harkokin kasuwanci da masana’antu, ya ce sabon shugabancinsu zai mayar da hankali wajen fadakar da ‘yan kasuwa muhimmancin aiki da kwararrun masana kididdigar kudi domin samun nasara a al’amuransu.

A yayin da yake gabatar da mukala Farfesa Kabiru Isa Dandago wanda kwarararen Malami ne a fannin, a jamiar Bayero ya bukaci kungiyar ta yi aiki da kwarewa wajen bunkasa tattalin arzikin jahar kano da harkokin kasuwanci dana masana’antu.

Wakilin Shugaban kungiyar na kasa Alh. Nasiru  da shugaban kungiyar ta ICAN reshen jahar kano mai barin gado Alh. Habibu Ayuba  da shugaban taron Ambasada Shu’aibu Ahmad da kuma Alh. Shehu Mohd Dankadai wadanda suka yaba da nagarta da kwarewar shugannin da aka zaba sun ja hankalinsu akan su kare martabar aikin Akanta musamman wajen rikon amana da gaskiya da kuma kare sirri a aiyukansu domin cigaban jahar, sannan sun yi fatan za su cigaba daga inda shubannin da suka gada suka tsaya.

FB IMG 1719815658439
ICAN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *