Yanzu haka mutum 17 ne ke kwance a asibiti suna samun kulawar likitoci yanzu haka.
Alfijir labarai ta ruwaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 11, yanzu haka.
An yi zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare damutum kusan 40 a ciki.
Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado
Tuni dai ‘yan sanda suka ce sun kama maharin mai shekara 38.
Lamarin ya faru ranar Laraba lokacin da mutane ke gabatar da sallar asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.
‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa ya aikata hakan ne da nufin ƙona wasu ‘yan uwansa da ke cikin masallacin waɗanda rigimar rabon gado ta shiga tsakaninsu.
“Abin da ya faru ba shi da alaƙa da ta’addanci, rigima ce da ta faru sakamakon rikicin rabon gado,” in ji Baturen ‘yan sandan yankin, Umar Sanda.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl