Ibtila’i: ’Yan bindiga sun ƙone wata makaranta bayan sun karɓi harajin N10m a Neja

FB IMG 1717835308108

Wasu ’yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare da ke garin Dekara a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa maharan sun ƙone Makarantar Firamare ta Central da ke Dekara lokacin da suka kai hari garin a ranar Laraba.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ’yan bindigar sun fito ne daga dajin Gandun Ƙasa na Tafkin Kainji kafin su mamaye garin.

A cewarsa, ƙauyuka da al’ummomin da ke Gundumar Dekara sun haɗa kuɗi Naira miliyan 10 domin biyan harajin da ’yan bindigar suka ƙaƙaba musu, bayan sun yi barazanar kai musu hari idan ba su biya ba.

Ya ce an biya kuɗin ne bayan ’yan bindigar sun yi alƙawarin cewa za su bar mazauna yankin su ci gaba da zama cikin garuruwansu ba tare da sake kai musu hari ba.

“Amma duk da sun karɓi kuɗin, sun sake kai hari hedikwatar gundumar tare da ƙona makarantar firamaren,” in ji shi.

A wani lamari mai alaƙa da wannan, an kuma ruwaito cewa ’yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a al’ummomin Dnakau da Lanta da Unguwan Kawo da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Mazauna yankin sun ce mutum ɗaya ya rasu, yayin da aka yi garkuwa da wani mutum guda a hare-haren.

An bayyana sunan wanda aka sace da Moses Joseph, mazaunin Unguwan Kawo, yayin da Emma daga ƙauyen Bagna ya mutu bayan an harbe shi a lokacin harin.

Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja bai yi nasara ba.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya ko saƙon tes da aka aika masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Trust Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *