Wata mummunar gobara ta tashi a wani gidan mai na Mobil da ke kan titin Obafemi Awolowo a Ikeja, babban birnin jihar Legas a safiyar yau, inda motoci da dama suka kone tare da jikkata wasu da dama.
Alfijir labarai ta ruwaito lamarin dai ya faru ne da safiyar Alhamis da misalin karfe 11, a daidai lokacin da masu ababen hawa ke kokarin shan mai a gidan man.
Shaidu sun ba da rahoton jin karar fashewar wani abu mai karfi a gidan man, inda nan take suka ga wuta ta tashi.
Gobarar ta cinye wata tankar man fetir, da motoci da dama, da kuma bas guda daya da ke cikin gidan man.
Ko da yake har yanzu ba a bayyana adadin wadanda suka jikkata a hukumance ba, an ce mutane da dama sun samu raunuka yayin da lamarin ya faru.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj