Ibtila’i! Ruwan Sama Ya Karya Gadar Da Ta Hada Bauchi Da Gombe

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi alkawarin bayar da duk tallafin da ake bukata domin a gyara gadar da ta karye a hanyar da ta hada jihohin Bauchi da Gombe a cikin mako guda.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Bala yayi wannan alkawarin ne a kauyen Kalajanga da ke Karamar Hukumar Kirfi a ranar Lahadi, a yayin da ya kai ziyarar tantance irin yankewar da hanyar ta yi sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da ya karya gadar.

Bala ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba aikin gyaran hanyar Bauchi zuwa Gombe zuwa Taraba da aka bayar tun a shekarar 2018.

Ya ƙara da cewa halin da hanyar ke ciki a yanzu yana da ban tsoro, musamman yadda ya jefa al’umma halin kunci, don ya yi kira da gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo dauki.

Ya ce hanyar ta hada shiyyoyin kasar nan guda uku na Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, don haka akwai bukatar a gyara ta domin rage yawan mace-mace da hadurran da ke faruwa a kan ta.

Gwamnan ya yi kira ga masu ababen hawa da ’yan kasa da su yi hakuri, tare da yin alkawarin kawo musu dauki ta hanyar hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin dakile illolin da rashin ta zai haifar.

Ya umurci babban Injiniya na jihar ya koma Kalajanga ya tabbatar da cewa ’yan kwangila sun bude hanyar cikin mako guda.

Ya ce alkawarin da dan kwangilar ya yi na gyara hanyar cikin kwanaki uku domin mai mota ya wuce ya ba shi kwarin gwiwa, ya kuma yi alkawarin mika wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima bukatar gyaran.

Dan kwangilar da ke kula da aikin, Injiniya Abraham ya yi alkawarin gyara hanyar cikin kwanaki uku, inda ya ce suna da isassun ma’aikata da injunan tabbatar da hakan.

Hakimin Kirfi, Alhaji Muhammad Lawal ya gode wa Gwamnan saboda ziyarar gaggawar da ya kai wa al’umma domin jajanta musu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *