Da Ɗumi Ɗuminsa: Tsohon Sufeton Ƴan Sandan Najeriya Ya Fito Takarar Sanata

Daga Aminu Bala Madobi

Ra’ayoyi mabanbanta sun fantsama biyo bayan wani hoton da ke nuna tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali-Baba, wanda ke nuna sha’awar sa a zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawan Yobe.

Alfijir Labarai ta rawaito hoton da ke dauke da alamar tutar jamiyyar ya fito a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, 2023, ya nuna Alkali-Baba mai taken Gobe Ta Allah Ce.

An lura cewa tsohon shugaban ‘yan sandan na iya neman tsayawa takarar kujerar Sanata a Yobe ta Kudu a karkashin inuwar jam’iyyar APC bayan da Sanata mai ci Ibrahim Geidam ya yi murabus domin zama minista.

Idan zaku iya tuna cewa Geidam, wanda shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Yobe ta Gabas a jihar Yobe, yana cikin kashi na biyu na sunayen ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya mika wa zauren majalisar a makon jiya.

A watan Yuni ne Tinubu ya kori Alkali-Baba bayan ya amince da ritayar dukkan shugabannin ma’aikatar tsaro da masu ba da shawara a nan take.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *