Gwamna Adeleke na jihar Osun da mukarrabansa sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin jirgin sama bayan jirgin da suka shiga, ya kama wuta daf da tashinsa.
Alfijir Labarai ta rawaito jaridar Leadership ta wallafa cewa, a ranar Talata, 5 ga Satumba, 2023, wani jirgi Bombadier Global Express 6000, mallakin hamshakin attajirin dan kasuwa, Cif Adedeji Adeleke, ya kama wuta a tashar tashin jirgin sama na Murtala Mohammed International Airport. MMIA) a Legas.

Cif Adeleke shi ne mahaifin mawaki, David Adeleke wanda aka
Fi sani da Davido, kuma dan uwa ne ga gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.
Lamarin ya faru ne a sashin gida na filin jirgin da misalin karfe tara na safe a daidai lokacin da jirgin ke shirin tashi daga Legas zuwa birnin tarayya Abuja.
Rahoton ya bayyana cewa jirgin da Gwamna Adeleke da mukarrabansa da ke cikin jirgin, an tuka shi ne zuwa karshen titin jirgin daf da tashinsa, sai aka ji karar fashewar wani abu daga injin jirgin.
Kafin tashin jirgin, an ajiye jirgin ne a babban ma’aikatar sufurin jiragen sama na Executive Jet.
Kazalika, Sam Iwuajoku, babban jami’in gudanarwa (CEO), Executive Jet wadanda suka mallaki hangar da aka ajiye jirgin mai zaman kansa, ya bayyana cewa jirgin na Cif Adeleke ya samu Lalacewar Abun Wuta (FOD) wanda ya sa jirgin ya yi zafi sosai, wanda ya haifar da fashewar.
“Lokacin da aka tashi, injin yana da zafi sosai, kuma ya faru ne sakamakon gida da tsuntsu yayi a daya daga cikin injinan jirgin, hakan zai iya haifar da zafi mai tsanani” In ji Sam Iwuajoku
Lamarin irin wannan ya faru da daya daga cikin jirgin sama na a 2021, dole ne muka cire injin kuma muka kai injin kasar Jamus tsawon watanni 14 ana gyaransa.

Don haka, abu ne gama gari a Afirka saboda muna da tsuntsaye a kusa, ”in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
Very nice and genuine story