Kaddarorin da aka kiyasta sun kai Naira miliyan 150, a ranar Talata, sun kone a kasuwar GSM, wadda aka fi sani da “Kasuwar Jagwal,” a Damaturu, Yobe.
Alfijir labarai ta rawaito jami in hulda da jama a na hukumar Kashe gobara ta Jihar Yobe yace akalla shaguna 30 ne gobarar ta lalata.
“Da misalin karfe 5:50 na safiyar yau, mun samu kiran gaggawa da ke sanar da mu lamarin. Bayan ‘yan mintoci kaɗan, tawagarmu ta isa wurin, amma an riga an yi barna da yawa a lokacin,” in ji shi.
Bello ya kara da cewa bincike ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki da aka samu a yankin.
Ya shawarci al’umma da su rika kashe na’urorin lantarki da kuma cire igiyoyinsu daga hanyoyin wutar lantarki kafin su yi barci ko rufe shagunansu na ranar.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Damaturu, Alhaji Ali Sheriff, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar kayayyakin da suka kai Naira miliyan 150.
Ya tabbatar da cewa watakila wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
“Da sanyin safiyar nan ne aka kira ni a kan abin da ke faruwa, kuma muka garzaya wurin da lamarin ya faru.
“Sai kuma, akwai shaguna kusan uku da suka kone. Jami’an kashe gobara suna wurin, amma lamarin ya fi karfinsu, don haka ba za su iya kashe wutar ba,” inji shi.
Ali ya ce jami’an ‘yan sanda suma sun kasance a wurin don taimakawa tare da hana satar kayayyakin ‘yan kasuwa.
Haka kuma wani mai sayar da dawa a kasuwar, Yahya Ngubdo, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar jimillar buhu 130 a sakamakon afkuwar lamarin.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su kawo agajin ‘yan kasuwar da abin ya shafa su rage musu asara.
NAN
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V