Ibtila’i! Gobara a wurin tace man fetur na sata ta kashe akalla mutum 18

FB IMG 1696341661273

Gobara a wurin tace man fetur na sata ta kashe akalla mutum 18 a ƙauyen Ibaa na karamar hukumar Emuoha da ke jihar Ribas.

Wani ganau a yankin ya faɗa wa gidan talabijin na Channels cewa gobarar ta auku ne lokacin da ɗaya daga cikin kwantenoni da ake zuba tataccen mai ya kama da wuta.

Ya ce ba a kai ga gano adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su ba, amma ana da yakinin cewa akwai mutane da dama a wurin.

Jami’an tsaro na Cibil Defence sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, inda suka ce mutum 18 sun mutu a lamarin.

Channels Television gathered that the incident occurred late Sunday night when some people in the community were scooping petroleum products.

Wata sanarwa da jami’an suka fitar, ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun ƙone kurmus.

Gobarar ta kuma jikkata mutum 25.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *