Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Kulle Gidajen Galar Dake Fadin Jahar Kano

FB IMG 1710082379852

A shirye-shiryen ta na shigowar watan Azumin Ramadana, Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jahar Kano ta bada umarnin kulle dukkannin gidajen Galar dake fadin jahar Kano.

Alfijir labarai ta rawaito wannan na zuwa ne biyo bayan wata ganawa da Shugaban Hukumar yayi da jagororin yan Kungiyar ta musu gidajen galar reshen jahar Kano a ofishin sa.

A cewar shugaban Hukumar Abba El-mustapha, dokar zata fara aiki ne tun daga yau lahadi har zuwa 1 ga watan shawwal wato ranar bikin karamar sallah.

Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji Karya doka domin duk wanda Hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika zata dauki tsastsauran mataki a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din.

El-mustapha ya kuma godewa jagorori tare da yan Kungiyar ta masu gidajen gala hadi da al’ummar jahar Kano dangane da hadin kan da suke bawa Hukumar a kowanne lokaci.

A karshe ya Kara tunatar da dukkannin al’umma cewa kofar sa’ a bude take domin bashi shawara ko sanar da Hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar aiyukan data saka a gaba .

Kamar yadda Abdullahi Sani Sulaiman jami’in Hulda jama’a na Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jahar Kano ya sanyawa hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *