Rundunar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta rahotan cewa jami’anta sun kai sumame shelkwatar kungiyar kwadago ta kasa NLC.
Alfijir labarai ta ruwaito bayanan DSS na zuwa ne bayan kungiyar kwadago ta zargi jami’an tsaron da kai sumame shelkwatar ta da ke Abuja.
NLC ta ce jami’an na DSS sun debi wasu takardu da suka ce da su aka yi amfani wajen zana jadawalin zanga-zangar #EndBadGovernance.
Acewar kungiyar, jami’an sun dira a ofishin ta da misalin karfe 8:30 na dare, inda ta ce “sun balle wajen ajiye takardu a hawa na 2 inda suka tafi da wasu takardu da mujalli”, acewar sanarwar da mai magana da yawun NLC, Benson Upah ya fitar.
Sai dai da ya ke mayar da martani, mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya ce ba jami’an su ba ne su ka kai samame ofishin NLC ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X na DSS, din, Ifunaya ya musanta kai samamen.
Kungiyar ta NLC ta yi Alla-Wadai da samamen inda ta nemi a gaggauta janye jami’an da su ke shelkwatar ta.
Channel
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj