Hasashen Yadda Siyasar Kano Zata Kasance a 2027 – Daga IPSA Bashir Gentile

IMG 20240125 172738

Yayin da aka fara shirye-shiryen tunkara babban zaɓen shekara ta 2027, tuni an fara hasashen yadda yanayin siyasar zai kasance.

Alfijir labarai ta rawaito IPSA Bashir Hayatu Jantile yayi hasashen cewa akwai kyakykyawan zaton za’a kulla tafiyar siyasa a tsakanin tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da shugaba Kasar Nigeria Tinubu.

Ana ganin Kwankwaso da yake jagorantar jam’iyyar NNPP idan suka hade da Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, saboda dimbin magoya bayan da yake da su a jihar kano, zai iya samarwa da Tinubu kuri’u wadanda suka zarce yawan kuri’un da jihohin Kudu maso Yamma suke samarwa a zaɓen shugaban kasa.

Sai dai kuma yanayin siyasar Kano a shekarar 2027 ya nuna cewa zai banbanta idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata

. Yanzu haka dai jihar na karkashin ikon wasu manyan ‘yan siyasa guda hudu, wadanda kowannensu zai iya cinye shiyya ko mazabarsa ga jam’iyyar siyasar da yake cikinta.

Kano ta Arewa tana karkashin Sen Barau Jibrin, Kano ta tsakiya kuwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ke da rinjaye, Kano ta Kudu kuma Sanata Kawu Sumaila ne ke jagorantarta, sai kuma rukunonin masu rike da sarautun gargajiya, malamai, ma’aikatan gwamnati, da masu fada aji a Kano su kuma suna karkashin Sanata Mallam Ibrahim Shekaru.

Don haka duk wata hadaka ta kungiyoyi biyu da muka ambata a baya da suka samu goyon bayan Sanata Mallam Ibrahim Shekaru zai yi tasiri a wannan yanayi.

Don haka ’yan siyasa ku yi hattara kada wasu ‘yan bangar siyasa su yaudare ku, Siyasar Kano a 2027 ba ta da tabbas.

Bashir Hayatu Gentile, MNIPR, MIPRA, MIPSAs, ARPA.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *