Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutun Cikar Kasar Shekaru 62 A Faɗin Kasar

Alfijr ta rawaito Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin bikin cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

Alfijr Labarai

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a lokacin da yake bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya ya taya daukacin ‘yan Najeriya murnar bikin tare da tabbatar da aniyar gwamnati na tinkarar dukkan kalubalen da kasar ke fuskanta tare da sanya murmushi a fuskokin jama’a.

Duniya na fama da matsalolin tattalin arziki da tsaro wadanda kuma suka shafi al’ummarmu.

Duk da haka, ina tabbatar mana da cewa gwamnati ba za ta yi watsi da jama’a ba, amma za ta ci gaba da tinkarar wadannan kalubale da dukkan karfinmu har sai an samu hutu,” in ji Ministan.

Alfijr Labarai

“Zamanin mu, ruhin mu da kauna da kuma jarin bil’adama mara iyaka da wadatar kasarmu, sun sa Najeriya ta zama babbar kasar bakar fata a duniya da kuma abin alfahari da bege na Afirka.

Idan za mu iya haɗa kanmu tare don yin amfani da damarmu, za mu zama al’umma mafi girma a duniya.

“Kasar da ke da mutane sama da miliyan 200 waɗanda basirarsu, ƙwaƙƙwaransu da sha’awarsu ke haskakawa kamar lu’u-lu’u mai daraja da muke;

Alfijr Labarai

‘Yan Najeriya suna kyalkyali kamar lu’u-lu’u a cikin kunshin, ko a fagen ilimi, kimiyya da fasaha, kasuwanci, kirkire-kirkire, wake, nishadantarwa, salo ko al’adu,” in ji Aregbesola.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *