Gwamnatin Najeriya Ta Maka Ƴan Kwadago A Gaban Kuliya Kan Zanga-Zanga 

Gwamnatin Nijeriya ta maka shugabannin Kungiyoyin ne a kotu saboda zanga-zangar da suka jagoranta a ƙasar kan tsare-tsaren gwamnatin da suke zargin sun jefa ’yan kasar a cikin halin kaka na kayi.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce an kawo musu sammacin kotun da cewa zanga-zangar ta ranar Laraba raini ne ga umarnin kotu.

Ya ce za su amsa kiran kotun amma hakan ba zai hana su gwagwarmayar samarwa al’ummar kasa saukin rayuwa ba.

Kunshin takardar kotun ta bayyana ‘Ana zarginmu da raina kotu, don haka muna kira ga ’yan Najeriya da su farga,” in ji shi.

Ya ƙara da cewar, za su ci gaba da jiran matakin da gwamnati za ta dauka kan bukatun da kungiyoyin suka gabatar mata ta hannun majalisa, wadda ta ba su tabbacin gwamnati za ta yi abin da ya kamata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *