Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallah

Alfijr ta rawaito Gwamnatin Najeriya ta ayyana Juma’a 21 da Litinin 24 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu, domin gudanar da shagulgulan bukukuwan karamar sallah 1444.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan harkokin cikin gida na ƙasar Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana a madadin gwamnatin tarayya.

Rauf ya kuma taya al’ummar musulmin ƙasar murnar kammala azumin watan Ramadan.

Ya kuma kara kira ga duk al’ummar musulmin ƙasar da su ci gaba da ayyukan alkairin da suka koya a cikin watan na Ramadan.

”Ina kira a gare ku da ku ci gaba da nuna wa juna halin dattaku, da soyayyar juna, da hakuri da juna da zaman lafiya da sadaukarwa da sauran kyawawan ayyuka, kamar yadda Annabi Muhammad S A W ya koya mana”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *