A kokarin da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamnan Dikko Umaru Radda take yi na ganin ta saukaka wa al’ummar jihar.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan jihar ya amince da a fitar da kudi Naira milyan 600 domin sayo karin motocin sufuri guda 40 ga hukumar sufuri ta KTSTA, ta yadda al’ummar jihar Katsina za su samu saukin tafiyar da lamurransu na yau da kullum.
Matakin ya biyo bayan taron majalisar zartarwa na jihar karo na biyu da ya gudanar a ranar Larabar makon nan 16th ga Agusta, 2023 a gidan gwamnatin jihar, Katsina.
Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Dr Sani Magaji Ingawa ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar.
Kwamishinan ya ce Mai Girma Gwamna ya umurci cewa za a yi amfani da motocin wajen sufurin ciki wa wajen jihar kamar yadda hukumar sufurin KTSTA ke gudanar da ayyukanta.
Dr Sani Sani Magaji Ingawa ya ce Gwamna ya kuma ce za a yi amfani da wani kaso na motocin domin daukar daliban makarantun firamare da na sakandare da ma na makarantun gaba da sakandare da ke jihar, duk don a saukaka musu wajen zuwa makaratunsu cikin lokaci.
Gwamnatin jihar ta sanar cewa ba za a tsawwala farashin hawa wadannan motoci ba, domin samun saukin Katsinawa su yi zirga-zirgarsu yadda ya kamata ba tare da takura ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM