Gwamnan jahar Kano ya aikewa da majalisar jahar Kano Dan Kwaryakwaryar kasafin kudi kimanin sama da (=N= 58b).
Alfijir Labarai ta rawaito Kasafin Kudin ya kunshi gina gadar Sama Data kasa a sha-taletalan Titin K/Dan’agundi da Tal’udu, Don rage cunkosan Ababen Hawa, anyi la’akari da Tituna ne dake da alaka da yawancin manyan makarantun gaba da secondary a jahar Kano.
Haka kuma Kasafin yana kunshe da harkar ilimi, wanda keda kaso mafi tsoka acikinsa, gyaran makarantun secondary da daukar nauyin ‘yayan jahar Kano zuwa karatu qasashen waje, wato digiri na biyu(Msc).
A harkar lafiya kuma, abubuwan da suka hada da gyare gyaren asubitoci dama Sanya na’urorin aiki na zamani, haihuwa kyauta da bada magani kyauta,, dasauran buqatu na bangaren lafiya.
Bangaren Auren Zawarawa! Don ragewa Al’umma radadi da cika musu burukan su na aiwatar da sunnar Annabinmu tsira (S.A.W). Dasauran manyan Ayyukan rayar da Al’umma.
Kamar yadda Chairman budget commitee na majalisar jahar Kano ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar na Yau Jumma’a
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb