Gwamnatin Kano Ta Nada Jami’an Alhazai Na Kananan Hukumomi

Alfijr ta rawaito gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da sake nada jami’an riko da za su gudanar da jigilar maniyyata aikin hajjin 2023 da ke gudana a fadin jihar.

A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yada labaran gwamnan ya fitar, ya umurci jami’an aikin hajjin na rikon kwarya da su karbe ragamar aiki daga waɗanda aka sauke.

Bayan haka, sanarwar ta umurci sabbin jami’an cibiyar da aka nada da su garzaya zuwa ofishin sabon Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano a yau Lahadi, 4 ga watan Yuni, 2023 don wani taron gaggawa a hedikwatar hukumar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *