Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Jita Jitar Rushe Masarautan Kano

Alfijir Labarai ta rawaito Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano H.E. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karyata cewar zasu cire Sarakuna.

Ya kara da cewa har yanzu ba a yanke shawara kan matsayin sabbin masarautun da tsohuwar gwamnatin ta kafa ba.

Sabanin jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta, gwamnatin jihar Kano ba ta dau wani mataki kan sabbin masarautun kamar yadda ake hasashe.

Tattaunawar tsakanin bangaren zartaswa da na ‘yan majalisar dokoki a Kano za ta kasance a bayyane domin baiwa mutanen Kano damar samun bayanai kan manyan manufofi da shawarwarin gwamnatin NNPP.

Sanusi ya ce mai girma Gwamna ya mika bukatar nada masu ba da shawara na musamman guda 20 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da su a zamanta na yau.

Ana sa ran za a aika da jerin sunayen sunayen kwamishinonin da za su yi aiki a majalisar mai zuwa domin tantancewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *