Daga AAbdul Ado K/Naisa
Abba kabir Yusuf ya Rantsar da masu Bashi shawara su Ar’ba’in da biyar Adakin taro na Africa House dake cikin gidan gobnatin jihar Kano,
Alfijir Labarai ta rawaito babban Antoni janar na jihar Kano Kuma komishnan sharia Barr, Haruna isa Dederi shi ya basu rantsuwa lokacin gudanar da taron*
A cikin jawabin sa Gamnan yayi kira gare su dasu kula da nauyin dake garesu wajan ciyar da jihar Kano gaba
Ya kara da cewa Kowannan su an zabo sune bisa cancanta da irin gudum nawar da suka taka Abaya wajan ciyar da jihar Kano gaba
Sannan yayi kira garesu Su zama masu biyayya ga ayyukan gwamnati, kuma suyi aiki tare da sauran ma’aikata don hada Karfi da karfe wajan samun cigaban jihar Kano
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb