Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Kano ya amince da naɗin Ibrahim Garba Shuaibu A Matsayin Sakataren yaɗa Labarai na mataimakin Gwamna Mai Girma Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ibrahim ya kammala karatunsa na adabi da turanci a jami’ar Bayero ta Kano.
Har zuwa lokacin da aka nada shi wakilin jaridar Thisday ne, kuma shugaban kungiyar ‘yan jarida a Kano.
Sauran wadanda aka nada a matsayin mukaddashin mataimakin gwamna sun hada da:
- Lawan Adamu Miko, babban mataimaki na musamman kan harkokin yarjejeniya
- Abubakar Tijjani Kura, babban mataimaki na musamman kan harkokin mulki
- Muhammad Garba Gwarzo, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa
- Abubakar Abubakar. Salisu Mijinyawa, mataimaki na musamman, na cikin gida
- Usman Nura Getso, mai taimaka masa a fannin mulki
- Hamza Ahmad Telan Mata, mataimaki na musamman, daukar hoto.
Kuma dukkan nade-naden na za su fara aiki nan take,
Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya sakawa hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
ALLAH YA TAYA RIKO