Gwamnan Kano Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Fansho

Habu

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Habu Muhammad Fagge a matsayin shugaban zartarwa na hukumar fansho ta jihar Kano.

Nadin ya fara aiki ne nan take kamar yadda gwamnan ya bayar da umarnin mikawa tare da karbar ragamar mulki cikin sa’o’i 24 da wannan sanarwar.

Alhaji Habu Fagge, wanda ya kammala karatunsa na BSc. daga Jami’ar Abraham Lincoln, ya yi wa’adi biyu a matsayin Shugaban hukumar tattara haraji na Cikin Gida a Kano.

Ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da suka hada da daraktan kudi, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga da darakta sauran haraji.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano H.E. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya wallafa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *