
Alfijr ta rawaito wasu bata-gari sun far wa tashar Kogi Radio 90.5 FM da ke Ochaja a Karamar Hukumar Dekina harin ne a safiyar Talata, inda bata-garin suka lakada wa masu gadin tashar dukan kawo wuka, sannan suka rika cin karensu babu babbaka, tare da kona muhimman kayayyaki.
“Bata-gari sun sace duk muhimman kayyayakin da ke tashar, har da wani janareto kirar Mikano wanda wani dan takarar gwamna a zaben da za a yi a watan Nuwamba ya bayar gudummawa, bayan da suka yi wa masu gadi duka kawo wuka”, in ji wani shaida.
Gwamnatin Jihar Kogi ta yi tir da harin, a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar yada labaran jihar, Salawu Patience, ta fitar, amma ta ba da tabbacin cewa jami’an tsaro na aiki don kamawa da kuma gurfanar da bata-garin domin hana maimatuwar hakan.
Ta ce kwamishinan ma’aikatar, Kingsley Fanwo, tare da Darakta-Janar na hukumar yada labaran jihar, Alhaji Ojo Oyila Ozovehe sun ziyarci tashar a ranar talatar domin ganin irin barnar da aka yi.
Ta bayyana cewa dole aka rufe tashar domin babu yadda za ta ia gabatar da shirye-shirye a haka, sakamakon irin barnar da aka yi a harin, amma gwamnatin jihar na kokarin ganin an farfado da tasar nan ba da jimawa ba.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ