Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, samar da ci gaba mai dorewa, tare da yin aiki kafada da kafada da kafafen yada labarai domin cigaban jihar.
Gwamnan, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta, ya yi wannan jawabi ne a yau Talata 12 ga Agusta 2025, a gidan gwamnatin jihar, yayin ziyarar ban girma da mambobin Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar na Kasa, Kwamared Alhassan Yahaya, su ka kai.
Ziyarar ta kasance cikin jerin shirye-shiryen taron NEC na NUJ da ake gudanarwa a Kano.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya, ya yaba da irin cigaban da aka samu a karkashin jagorancin Gwamna Yusuf, yana mai cewa cigaban “mai inganci ne kuma abin burgewa.”
Ya bayyana cewa zabar Kano a matsayin wurin taron NEC na NUJ na wannan karo ba wai da-ka aka yi ba, sai domin mambobin su gani da idonsu irin sauye-sauyen da ake samu a jihar ne ya janyo hakan.
Ya ce: “Mambobinmu sun zo ne domin su ga ayyukan ci gaba da kansu. Shaidun da suka bayar sun isa su bayyana gaskiya.” ya kuma tabbatar da a tarihin NUJ ba a taba taron NEC da ya kai wannan tsaruwa da haduwa ba.
Shugaban NUJ ya kuma nuna godiya ga gwamnan bisa kyautar babura guda 11 da buhunan shinkafa 450 ga ‘yan jarida a Kano, da kuma yadda aka karbi bakuncin taron NEC na kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa (NAWOJ) a baya.
Kafin Ziyarar dai sai da Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Waiya, ya jagoranci Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) na kasa, Alhassan Yahaya, da sauran yan tawagarsa a wani rangadin duba wasu daga cikin hanyoyin da aka kammala da kuma wadanda ake ci gaba da ginawa.
Waiya ya ce, Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da kwangiloli fiye da Naira biliyan 40.8 domin gina sabbin hanyoyin cikin birni guda 17 a kananan hukumomi da ke cikin birnin Kano.
Hanyoyin da aka kaddamar da kwangilarsu sun shafi kananan hukumomi kamar Gwale, Nasarawa, Kumbotso, Fagge, Kano Municipal, Tarauni, Dala da Ungogo.






Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t