Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kwashe illahirin masu larurar ƙwaƙwalwa da ke gararamba a kan titunan jihar a birni da ƙauye.
Alfijir labarai ta rawaito Fauziyya D Sulaiman, hadima ta musamman ga Gwamnan kan harkokin jin-ƙai ce ta shaida hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na facebook a yau Talata.
Ta ce gwamnan ya bada umarnin ne bayan koke-koken da al’umma su ka shigar ga gwamman.
Ta kara da cewa tuni dai aka fara aikin kwashe masu larurar zuwa asibitlcin masu larurar ƙwaƙwalwa domin kulawa da lafiyar su.
“Bayan koke-koke da aka shigar gurin Gwamnan Abba Kabir Yusuf akan masu larurar kwakwalwa da ke yawo akan titunan Kano cikin birni da kauye wasunsu ma tsirara suke yawo, wasu ana cutar da rayuwarsu musamman mata, kuma ba su da galihun da zaa dauke su akai su asibiti, mai girma Gwabna ya bayar da umarnin a kwashesu akai su Asibitin masu Larurar kwakwalwa domin kulawa da lafiyarsu.
“Yau muka fara wannan aikin karkashin hukumar Agajin gaggawa (SEMA) da kuma office dina, SSA Needy and Valnurble,” in ji ta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp