Gwamna Ganduje Ya Tabbatar Da Zai Saka Hannu A Rataye Mal Abduljabbar

Alfijr ta rawaito Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce yana kan bakarsa game da sanya hannu kan hukuncin rataya da kotun Musulunci ta yanke wa Abduljabbar Kabara kan batanci ga Manzon Allah (SAW).

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Lawan Musa, ne ya sanar da haka, bayan Aminiya ta tuntube shi kan hukuncin da Babbar Kotun Musulunci ta yanke wa malamin da gwamnatin jihar ta gurfanar kan zargin batanci.

Ya ce, “Matsayin gwamna bai sauya ba kan sanya hannu a kan wannan hukunci, kamar yadda matsayin bai sauya a kan hukuncin Kisan Hanifa ba.

“Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye Mai Girma Gwamna yake; da zarar an kawo zai sanya hannu a kai,” in ji shi.

Kwamishinan Shari’an ya kara da cewa, “Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakan da suka kamata.

“Mun gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu ne domin ba shi duk wata dama ta kare kansa, kuma Alhamdulillahi kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar a kansa, sannan ta yanke masa hukuncin da ya cancanta.”

A cewarsa, hukuncin kotun ya wanke gwamnatin jihar kuma ya nuna babu wani shafaffe da mai, sannan gwamnatin ta dauki duk matakan da suka dace na tabbatar da doka da oda.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

One Reply to “Gwamna Ganduje Ya Tabbatar Da Zai Saka Hannu A Rataye Mal Abduljabbar”

  1. Allah Azza Wa Jallah!

    Allah shi kadai ne ba Wanda ya Isa ya ja da shi ko yaja da manzoninsa, littattafensa (Al-qur’ani, Attaura da Linjiila) ko mala’kunsa. Idan kuwa ka gwada, kaga abinda zai biyo baya.

    Allah ka tabbatar mana da cikan imanin mu.

    Ya Allah ka kara karfafa zuciyar mu ta tsorace ka domin bin umarnin ka Ya Allah, amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *