Gwamna Ganduje Ya Nada, Tare Da Shirin Rantsar Da Babbar Alkalin Alkalan Jihar Kano

Alfijr ta rawaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin mai shari’a Dije Abdu Aboki a matsayin babban alkalin alkalan jihar, a matsayinsa na riko.

Nadin mai shari’a Aboki ya biyo bayan ritayar tsohon babban alkalin alkalai, Justice Nura Sagir ne.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Mallam Muhammad Garba, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce kafin nadin nata, Mai shari’a Aboki ta kasance alkalin babbar kotun jihar tun shekarar 2006.

Mai shari’a Dije ta kammala karatun shari’a a babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 1983.

A shekarar 1984 ne aka kai mai shari’a Aboki zuwa hukumar shari’a,” in ji sanarwar.

Ta fara aikinta na lauyan gwamnati ne a shekarar 1985 a karkashin ma’aikatar shari’a ta jihar inda bayan shekara daya aka nada ta a matsayin Majistare, kuma ta zama alkaliyar babbar kotu a shekarar 2006.

”Ta kasance mamba ce ta kwararru daban-daban, ta kuma ta rike mukamai da dama.”

Sanarwar ta ce nadin nata ya fara aiki nan take, za a rantsar da ita a yau Alhamis

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *