Gaskiyar lamari tsakanin Gwamna Kabiru Gaya da Gwamna Rabiu Kwankwaso—Waye ya Kafa Jami’ar Wudil

IMG 20250511 190613

Daga Aminu Bala Madobi

Batun cikin tsaffin Gwamnonin Kano wanene ya Kafa Jami’ar Wudil na cigaba da daukan hankali, inda ya zamo abin tattaunawa da ya karade shafukan sada zumunta. Ana ta muhawara game da ainihin wanda ya assasa jami’ar farko mallakar jihar Kano, wato Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote.

Dalla Dalla.

A lokacin Jamhuriyya ta Uku ke cin sharfin ta, daga bisani sojoji suka hambarar, gabanin haka, an rantsar da Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya a matsayin Gwamnan Jihar Kano a watan Janairun 1992, wanda ya gaji Kanar Idris Garba, wanda yanzu haka yake Manjo Janar Idris Garba mai ritaya, ya zama Gwamnan Jihar Kano.

Lokacin da Kabiru Gaya ya zama Gwamna, zai yi wuya gan sa a gurin tarurrukan jama’a ba tare da ka ji ya ce “Insha Allahu ba,” ma’ana “da yardar Allah” — jumlar da kowanne musulmi ake kwadaitar da shi ya fadi kafin ya fara wani aiki na duniya.

Masu nazari kan al’amuran yau da kullum da sha’anin siyasa a lokacin sun fahimci cewa mafi yawan maganganu da alkawuran da Gwamna Kabiru Gaya yayi a jajibirin rantsar da shi bai cika su ba har zuwa lokacin da sojoji suka karbe mulki a ranar 17 ga Nuwamba 1993.

Misali, a ranar da aka rantsar da shi Gwamna Kabiru Gaya ya shaidawa al’ummar Kano a filin sukuwa na Race_course cewa zai gina katafaren filin wasa. Kabir Gaya har ya bar gidan gwamnati, wannan alkawarin bai taba cika ba.

Ya kuma yi alwashin ganin an rika raba fasinjoji maza da mata acikin ababen hawa; a wancan lokacin babbar hanyar sufuri a Kano da kewaye ita ce motar Hiace. Wannan alkawarin shi ma kuma bai aiwatar da shi ba.

A lokacin jihar Kano da ke makwabtaka da ita, sabuwar Jihar Jigawa, karkashin matashin Gwamnan ta, Ali Sa’adu Birnin Kudu—wakilin Alhaji Sule Lamido— bai yi kasa a gwiwa, ya bada himma sosai wajan aiwatar da ayyuka da dama. Daga cikin su akwai kafa gidan rediyo na farko a Jigawa, wanda za a iya sauraran sa anan Kano, da kuma gina gidaje 1,000 da ake kira Gida Dubu a unguwar Takur a babban birnin jihar.

Daga nan ne mutanen Kano suka fara habaici ga gwamnan su da taken: “Insha Allahu na Kano, Aiki na Jigawa,” ma’ana, “An yi shelar nufin Allah a Kano, yayin da a Jigawa ake ta gudanar da ayyuka a aikace, ma’ana, anata surutu a Kano amma aiki na Jigawa.

To Ya Batun Yake? Wa Ya Kirkiro KUT

A shekarar 1992, Duba da yawaitar jami’o’in gwamnati a yankin kudancin Najeriya, sai jihohin Arewa suka fara bin kwaikwayon yadda anan Arewa su ma zasu motsa domin a dama dasu. A waccan lokacin, Rabaran Moses Adasu, tsohon gwamnan jihar Binuwai, a lokacin jamhuriya ta uku da aka soke, ya samu lasisin kafa jami’ar jihar Binuwai—kamar yadda Gwamna Kabiru Gaya, dake mulkin Kano a karkashin jam’iyyar NRC, ya samu makamancin wannan lasisi daga hukumar jami’o’i ta kasa don kafa jami’a ta farko a jihar Kano.

Rahotonni sunce, A gurin Gwamna Kabiru Gaya abin ya sha banbam, Shi Rabaran Moses Adasu, baya ga samun lasisin don kafa jami’ar jihar Binuwai, ya jajirce ya tabbatar da jami’ar ta fara aiki nan take, tare da samar da tsare-tsare da kuma gudanar da ayyuka, komai ba ilimi ya kankama a Jami’ar.

Sabanin haka, ga Jami’ar Jihar Kano, baya ga samun lasisin, babu wani abu sabo da akayi tun bayan samun lasisin na amincewa a kafa a Jami’ar har zuwa lokacin da sojoji suka hanbare  Gwamna Kabiru Gaya ya bar ofis da lasisin kawai.

Bincike ya nuna cewa a shekarar 2001—kimamin shekaru takwas bayan Jami’ar Jihar Binuwai ta yaye dubban dalibai masu tarin yawa— Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a wa’adinsa na farko, ta ya gabatar da dukkan tsare tsare da yin abun da ya dace domin asassa Jami’ar ta fara aiki wanda tuni takwarar ta daga Benuwe ta fara aiki tsawon shekaru 8. Gwamna Kwankwaso ya bada umarni a fara gudanar da harkokin ilimi cikin gaggawa.

A yau, Jami’ar Wudil ta shafe shekaru 24 tana aiki, yayin da Jami’ar Jihar Binuwai ta shafe shekaru 33 tana aiki, wannan ya nuna tsaikon da aka samu na rashin fara aikin Jami’ar akan lokaci da takwarar ta ta Benuwe ya sa shekarun fara aikin Jami’ar ya banbanta.

Kabir lasisi kawai ya nemo, kuma tun daganan bai kuma yin komi akan maganar Jami’ar ba, har lokacin da sojoji suka soke jamhuriyya ta 3 a 1993.

Don haka, tsakanin Gwamna Kabiru Gaya da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, wanene a zahiri ya kafa Jami’ar Jihar Kano ta farko?

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *