Ganganci: Wani ɓarawo ya kwanta dama yayin satar wayar Lantarki

Wani ɓarawo da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya mutu sakamakon jan wutar lantarki a kusa da ginin tsangayar ilimi da ke kusa da sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Nnamdi Azikiwe Awka, jihar Anambra.

Alfijir Labarai ta rawaito wanda ake zargin barawon na USB ya gama yanke wayar daga falwaya kenan, kwatsam sai kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu ya dawo da wuta.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.

An ga gawar matashin na reto a kan sangalalin falwayar a safiyar jiya Laraba, inda aka ga ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki suna ƙoƙarin sauko da gawar ta sa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa jami’an rarraba wutar lantarki, ƴansanda, da jami’an sashen tsaro na jami’ar ne su ka sauko da gawar.

Wani ma’aikaci a jami’ar da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya ce, “Mun zo da safe ne muka tarar da gawar na reto a jikin taransifoma da ke yankin sabon ginin Kwalejin Ilimi, kusa da sashen ilimin tattalin arziki.

“Shaidu sun nuna cewa ya kammala yanke wayar kenan sai aka kawo wuta, shine fa ta kama shi,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *