Burkina Faso ta sha alwashin kare Nijar daga katsalandan na kasashen waje.
Alfijir Labarai ta rawaito Burkina Faso ta aika wa Nijar manyan motoci 265 cike da kayayyaki, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Nijar (RTN) ta bayyana ranar Alhamis.

Ministan Kasuwanci da Masana’antu Seydou Asman ne ya je ofishin Hukumar Kwastam na yankin Yamai da Tillabery don karbar kayayyakin da Burkina Faso ta kai wa Nijar gudunmawa.
Taimakon wani bangare na agajin muhimman kayan yau da kullum da kasar ta yi alkawarin bai wa Nijar bayan ECOWAS ta sanya wa kasar takunkumai sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Wannan ne taimako na biyu da aka kai wa kasar a cikin watanni. Sai dai ba a san hakikanin abin da gudunmawar ta kunsa ba, a cewar rahotanni.
Le Ministre du Commerce et de l’Industrie était hier en fin d’après midi dans les locaux de la Direction Régionale des Douanes Niamey – Tillabéry.
Seydou Asman est allé constater l’arrivée de 265 camions de marchandises diverses en provenance du Burkina Faso ⤵️ pic.twitter.com/WzRX4U25sP— RTN Niger (@rtnniger) September 13, 2023
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanya takunkuman karya tattalin arziki a kan Nijar, tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, ciki har da rufe iyakokin kasar da dakatar da huldar kasuwanci da kasar wadda ba ta da teku.
Har ila yau kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar soji wadda za ta bai wa Burkina Faso damar tura sojojinta da makamai Nijar don mara mata baya idan ECOWAS ta yi amfani da karfin soja a kan jagororin juyin mulkin kasar.
ECOWAS ta ce a shirye take ta yi amfani da dakarunta da ke cikin shirin ko-ta-kwana wajen da dawo da hambararren Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki idan aka gaza shawo kan lamarin ta hanyar diflomasiyya.
Sai dai Nijar ta sha alwashin mayar da martani cikin hanzari kuma mai karfi kan duk wani kutse daga kasashen waje. Burkina Faso da Mali sun yi alkawarin mara mata baya.
An tura dakaru kan iyakar Benin
A gefe guda, sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun tura dakarunsu yankin da ke kan iyakar kasar da Benin ranar Laraba, a cewar rahotannin kafafen watsa labarai na kasar.
Hakan na faruwa ne kwana guda bayan sun yanke huldar soji da ke tsakaninsu da makwabciyar tasu, suna masu zarginta da bari a yi amfani da kasar domin jibge sojoji da kayan yakin da ECOWAS za ta yi aiki da su don yiwuwar kai musu hari.
Hotunan da wasu kafafen watsa labaran kasar suka wallafa, wadanda ba mu tantance sahihancinsu ba, sun nuna yadda mazauna yankin suke maraba da zuwan dakarun.
TRT Afrika
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb