Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta kama wasu mutane 24 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo a Kano, a wani samame da ta gudanar ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.
Jami’an hukumar na reshen Kano sun gudanar da aikin ne a kusa da Jami’ar Bayero Kano (BUK), bayan samun sahihan bayanai game da yadda ake zargin matasan da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo. Dukkan wadanda aka kama daliban Jami’ar Bayero Kano ne.
Kayan da aka samu a hannunsu sun hada da wayoyin salula, kwamfutocin tafi-da-gidanka, na’urorin samun intanet da mota kirar Honda Accord.
Wadanda aka kama sun hada da Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan, Abubakar Abusufyan, Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid.
EFCC ta ce samamen ya biyo bayan makonni na bincike da ya nuna alaka tsakanin wadanda ake zargin da damfara ta yanar gizo, satar bayanan sirri da kuma zamba ta kudi.
Hukumar ta kara da cewa za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t