EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Matasa Gaban Mai Shari’a Saboda Zamba Ta Internet

Alfijr ta rawaito hukumar EFCC reshen jihar Kwara, Ilorin ranar Litinin 14 ga watan Maris, 2022 ta samu nasarar yankewa wasu mutane shida hukunci a gaban mai shari’a, saboda laifuka masu alaka da zamba ta intanet, sojan gona.

Wadanda ake tuhuma sun hada da Adeshina Wasiu, wani mai walda a Offa, sai Hammed Akorede mai shagon aski a Offa, sai Komolafe Shina David daga karamar hukumar Ilesha ta gabas, jihar Osun; sai Fatimehin Kayode daga karamar hukumar Ekiti jihar Kwara; sai Adetoye Damilare Timilehin daga karamar Boluwaduro, jihar Osun da Adebayo Ridwan Abiola dake karamar hukumar Obokun , jihar Osun.

EFCC ta gurfanar da su a gaban mai shari’a Muhammed Sani na babbar kotun tarayya dake Ilorin sannan sun amsa laifukan da ake tuhumar su.

Alfijr

Kotu ta yankewa Wasiu hukuncin wata shida ko tarar dubu dari biyu sai Hammed zai yi zaman watanni shida ko tarar dubu dari. Komolafe zai yi zaman wata shida a kowacce tuhuma uku da ake masa ko ya biya tarar dubu dari da hamsin.

Fatimehin zai zaman watanni shida ko tarar dubu hamsin sai Adetoye zai zaman watanni shida ko tarar dubu dari biyu inda Adebayo zai zaman gidan gyara halinka na watanni shida ko tarar dubu dari.