Dubun Barawon Adaidaita Sahu Da Safarar Mutane Ta Cika A KAno

Screenshot 20240522 131358 Facebook

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Kano, ta ce ta ceto mutane 13 da aka yi fataucin su a jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito kwamandan NSCDC na jihar Kano Mohammed Lawal-Falala, ya bayyanawa manema labarai haka.

Ya bayyana cewa an ceto mutanen ne a ranar 20 ga watan Mayu a unguwar Dan Tsinke da ke karamar hukumar Tarauni Kano.

A cewarsa, NSCDC ta samu labarin cewa wani mutum ya ajiye yara mata a gidansa yana safarar su zuwa Kamaru.

Falala ya ce jami’an hukumar sun kama daya da ake zargi da ajiye wadanda za ayi safarar su a gidansa, yayin da ake tsare da wasu mutane biyu.

“Wadanda aka ceto sun hada da mata biyar, kanana yara mata uku, namiji daya da maza hudu, wadanda aka ceton suna kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri a kan hanyarsu ta zuwa kasar Kamaru domin yin aikin kwadago”.

Kwamandan ya yi nuni da cewa za a mika wadanda abin ya shafa ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), domin daukar matakin da ya dace.

“A cikin 13 da abin ya shafa, 10 ‘yan Kano ne, uku kuma ‘yan jihar Jigawa ne.

Hakazalika, rundunar ta kuma kama wani da ake zargi, wanda ya kware wajen satar Baburamasu kafa uku da wayoyin hannu.

Falala ya ci gaba da cewa, mutane da dama sun ziyarci ofishin NSCDC don korafin satar babura masu kafa uku.

Ya yi nuni da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike.

Da yake zantawa da manema labarai, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya saba badda kama kamar ya samu karaya a kafarsa tare da daure ta da bandeji sannan ya hau adaidaita sahu tare da abokansa, kafin aikata aikata aikarsa

“Ni da abokaina za mu yi hayar adaidaidata sahu kuma idan muka isa inda muka nufa, za mu karkatar da adaidaita din kuma mu yi amfani da maɓallin mu mu sace shi.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *