Wasu daga cikin wadanda ake zargin da aka kama a wata shahararriyar kasuwa da ke garin Lafiya
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sanar da kama wasu jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Nassarawa, suna karkatar da kayan abinci da nufin dakile agajin cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya.
Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Talata, 5 ga Satumba, 2023.
A cewarsa, wasu daga cikin wadanda ake zargin da aka kama a wata shahararriyar kasuwa da ke garin Lafiya inda ake sayar da kayayyakin sun hada da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Nasarawa (NASEMA) da sauran abokan aikinsu.
Afunanya ya bayyana cewa an kwato wasu daga cikin kayayyakin da aka karkatar daga hannun wadanda ake zargin.
“Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu rahotanni daga wasu gwamnatocin Jihohin da abin ya shafa kan karkatarwa ko siyar da kayan abinci da aka tanadar wa ‘yan kasarsu,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM