Kotun ta ci tarar mai shigar da karar Naira N200,000.
Alfijir Labarai ta rawaito Kotu ta yi watsi da karar da Umar Abdullahi Ganduje, na jam’iyyar APC ya shigar a gabanta na kalubalantar nasarar Tijjani Abdulkadir Jobe na NNPP a zaben majalisar wakilai ta tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Maris. 2023.
Alkalin kotun, ya yi watsi da karar sabida rashin cancantarta.
Kotun ta bayyana cewa, mai shigar da kara ya kasa gabatar da isassun shaidu da za su tabbatar da zargin da ya yi a yayin gudanar da zaben.
Kotun ta ci tarar mai shigar da karar Naira N200,000.
For More information you can join us on
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Group Whatsapp Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM