Alfijr ta rawaito Kotun Majistare mai lamba 14 ta aike da wani alkali da ma’aikatan Hukumar Shari’a gidan gyaran hali saboda zarginsu da wawure Naira miliyan 99.
Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wasu Marayu.
Hukumar Karbar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotun.
Sani Ali, Sani Uba Ali da Bashir Baffa, Gazzali Wada na daga cikin wadanda ake tuhuma, sauran sun hada da Hadi Tijjani Mu’azu, Alkasim Abdullahi tare da Yusuf Abdullahi, Mustafah Bala, da Jaafar Ahmad, Adamu Balarabe, da kuma Aminu Abdulhadi, ragowar sun hada da Abdullahi Sulaiman Zango, Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa tare da Usaina Imam, sune mutanen da suka gurfana a gaban Kotun.
Kunshin karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan kotun shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira miliyan 99.
Wadanda ake zargin duk sun Musanta laifukan bayan karanta musu.
Barista Zaharaddin Kofar Mata shine mai gabatar da kara, ya roki kotun da ta sanya wata ranar domin sake gabatar da shaida.
A nasu bangaren lauyoyin wadanda ake kara sun nemi da mai shari’a ya basu beli, amma kotun tayi kemagadas ta hana bayar da belin nasu.
Mai shari’a yace a zama na gaba kotu za ta bayyana matsayinta game da rokon belin da aka yi mata, a ranar daya ga watan Fabrairu, 2023.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
To Allah ya kiyaye cin kudin marayu tab
Ina so abani data 500MB
Ya kamata ma a kashe su tunda suna son chin amanar aluma kasa
Wallahi kuwa