Alfijr ta rawaito Wani dan uwan gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Amadu Ali, da ‘yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da ayarin motocin gwamnan.

Babban Darakta na Social Media na Masari, El-Amin Isa, da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, sun tabbatar da faruwar hatsarin, wanda ya faru a ranar Juma’a.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wadanda abin ya shafa tare da wasu, na kan hanyarsu ta zuwa mahaifar gwamnan, Kafur, domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar da za a yi ranar Asabar.
Majiyoyin sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon Mummunar rashin kyan hanya da aka fama da shi a yankin.

Wata majiya ta ce, “Wadanda lamarin ya rutsa da su sun kusa isa wata gada da ke yankin ne a ranar Juma’a da daddare, sai suka fada wani rami a hanyar, lamarin da ya tilasta wa motar da suke ciki ragargajewa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Wasu 3 da suka samu raunuka a hatsarin, an garzaya dasu domin Samun kulawa a babban asibitin Malumfashi, kafin a kai su asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Katsina.
Tuni dai aka fara shirye-shiryen binne su a ranar Asabar, kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya ce an dauke gawarwakin fasinjojin da suka mutu daga wurin zuwa dakin ajiyar gawa a Katsina.
Isah ya ce, “Hatsarin ya faru ne a daren Juma’a.

Wadanda abin ya shafa dai sun je Kafur ne, mahaifar gwamnan domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha. Mun kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Katsina.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Ubangiji Allah yajikanshu