Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ce ta barshi ba shine ya barta ba.
El-Rufai a hira da yayi da DW Hausa, ya zargi jam’iyya mai mulki ta APC da yi masa rufa-rufa da balesu da hayaki bayan sun tura motar ta tashi.
Daganan sai ya kara da cewa ” Ko ɗa ne kake da shi ya ki yi maka biyayyaka yi masa komai amma ya ki biye maka, za ka tsine masa kabarshi da duniya, haka APC, na tsine mata na barta da duniya.
Game da ziyarar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna, El-Rufai ya ce bayan sun tafi ne shima shugaban APC Abdullahi Ganduje ya kai wa tsohon shugaban ziyara.
” Ai ziyarar Ganduje ga Buhari neman suna ne kawai da iyayi, amma ba shine ya ke yi wa Buhari shaguɓen ‘Habu Na Habu ba’ ya rika yi masa ‘izgilanci’ amma yanzu wai ya ziyarce shi.
El-Rufai ya ƙara da cewa ya zaɓi jam’iyyar SDP ne saboda ta na da manufofi irin na taimakon al’umma da talakawa.
“Jam’iyyar SDP ta yi kama da irin jam’iyyar da za mu yi tafiya a ciki domin taimakon talakawa da mutanen mu na Arewa musamman da ƙasa baki ɗaya
El-Rufai tare da wasu gaggan ƴan jam’iyyun adawa na shirin dagula wa jam’iyya mai mulki kissafi a wata sabuwar tafiya wanda suka kira sabuwar goguwar canji.
PREMIUM TIMES
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD.