Alfijr ta rawaito jagoranci dalibai, ƙarƙashin ƙungiyar dalibai ta kasa, NANS, ta rufe hanyoyin da ke zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Lagos
Alfijr Labarai
Lamarin zanga-zangar wani mataki ne na nuna adawa da matakin yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i ke yi, yadda shuwagabanni suka ki maida kai wajen satin dai daito
Daliban sun fito duk da yanayi ruwan sama da ake kamar da bakin kwarya,an sun jure sun fito, inda su ka haifar da cunkoson ababen-hawa a titin da ke kan hanyar zuwa filin jirgin, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale.
Lamarin ya faru ne a ifom jami’an rundunar ƴan sandan jihar Legas, da jami’an RRS, da na ‘yan sandan filin jirgin saman Legas, da sauran jami’an tsaro suna nan suna kallon ikon Allah
Alfijr Labarai
Ɗaliban da suka gudanar da zanga-zangar na dauke da alluna da kwalaye, su na ta rera wakokin gwagwarmaya domin nuna rashin jin dadinsu kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.
The Nation