Babbar kotun tarayya da ke Apo a Abuja ta ba da umarnin kwace kadarori da darajarsu ta kai kusan naira biliyan 8.94 da ake dangantawa da fitacciyar ‘yar kasuwa kuma shugabar kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Ltd., Aisha Achimugu.
Mai shari’a Jude Onwugbuzie ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shigar da bukatar neman a kwace kadarorin har abada.
Kadarorin da kotun ta ba da umarnin a kwace sun hada da kayan ado na mata masu darajar kusan naira biliyan 4.65, motoci 11 masu tsada da darajarsu ta kai kusan naira biliyan 4.29, tare da dalar Amurka $50,000 da kuma tsabar kudi naira miliyan 30.
EFCC ta bayyana wa kotun cewa kadarorin na da alaka da binciken da take gudanarwa, inda ta nemi a mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.
Bayan nazarin bukatar, kotun ta amince da rokon EFCC tare da bayar da umarnin kwace dukkan kadarorin zuwa hannun Gwamnatin Tarayya.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
