Gwamnatin jihar kano ta sanar da dage dokar hana fita da ta sanya sakamakon yadda zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Abaya gwamnatin jihar kano ta sanya dokar ne tun a ranar Alhamis ranar farko kenan da fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa bayan wasu bata gari sun fake da zanga-zangar su ka rika fasawa da sace kayan gwamnati da na al’umma.
Kwamishinan yada labarai na jihar kano Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.
Yace gwamnatin ta dauki wannan matakinne sakamakon yadda al’amura suka koma daidai, zaman lafiya ya dawo jihar yadda ya dace.
Hakan dai yana nufi an dage dokar kwata-kwata a kwanaki masu zuwa, mutane za su iya cigaba da harkokinsu na yau da kullum.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj