Alfijr
Alfijr ta rawaito an gano kwalaben ruwan mai tsaron ragar Masar da bayani kan fitattun masu cin fenareti na Senegal
Alfijr
An gano kwalbar ruwan na golan Masar, Gabaski, wanda ke kunshe da abubuwan da ‘yan wasan Senegal suka fi so a kan tsarin bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Bayan kammala wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a Kamaru, an tashi wasan karshe ne tsakanin ‘yan wasan Teranga Lions na Senegal da Masar da bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda Mane ya samarwa Senegal nasara a karshen wasan, bayan da farkon wasan ya barar da bugun fanareti.
Alfijr
Bayanansa da aka manna a cikin kwalbar, wanda ya yi nazari sosai kafin kowane fanareti, Gabaski ya bi hanyar da ta dace amma sau daya kuma ya ceci bugun daga kai sai mai tsaron gida da Sadio Mane ya yi a daidai lokacin.
Alfijr
Sai dai kash kokarinsa ya kasa baiwa Masar kofin, a rahoton da jaridar Daily Mail ta wallafa.