Alfijr ta rawaito Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Ya lashe kyautar ‘INNOVATIVE LEADER AWARD’ a karo na biyu na ilimi na duniya da kuma EdTech Conclave and Awards 2023.
An gudanar da taron ne a New Delhi India A ranar 19 ga Janairu 2023
Babban dalilin da aka bayyana domin lashe wannan lambar yabo, ya hada da Kafawa da gudanar da katafariyar Jami’ar Maryam Abacha American University MAAUN da ke Nijar da Najeriya.

Hakazalika tare da fito da sabbin hanyoyin aiwatar da ayyuka masu tasiri a gidauniyar AAG.

A madadin hukumar gudanarwa da ma aikatan jaridar Alfijr, muna taya Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo murnar samun wannan gagarumar Nasara gareshi da al’ummar Najeriya baki daya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇