Alfijr ta rawaito wasu matasa daya mai shekaru 17 dayan mai shekaru 27, sun rasu a wani ramin masai a Kasuwar Sabon Garin Kano Ƙaramar Hukumar Fagge, jiya Asabar, yayin da ya bude ramin.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a Kano a yau Lahadi, inda ya ce hatsarin ya faru ne cikin dare.
Saminu ya cewa matashin mai shekaru 27 a duniya yana aiki ne a cikin ramin lokacin da ya makale, a kokarin ceto shi abokin aikinsa ya shiga cikin babban ramin shi ma ya makale cikin sa.
“Mun sami kiran gaggawa a kan hatsarin kuma nan da nan mu ka aika da tawagar ceto zuwa wurin,” in ji shi.

Ya kara da cewa hukumar kashe gobara ta fitar da matasan a sume, inda su ka kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammad, likitocin da ke bakin aiki su ka tabbatar da mutuwar su.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa an mika gawarwakin ga ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari.
Saminu ya danganta mutuwar mutanen da yawan zafin cikin ramin da kuma rashin iska
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇