Da Ɗumi Ɗuminsa: Wani Hatsarin Jirgin Sama Ya Faru A Filin Jirgin Sama Na Abuja

Alfijr ta rawaito Wani jirgin saman Max Air ya yi hadari bayan da rahotanni suka ce tayar ce ta kama da wuta ta kama.

Jirgin dai ya taso ne daga Yola jihar Adamawa lokacin da lamarin ya faru.

Jami’an hukumar ceto da kashe gobara (ARFFS) a filin jirgin sun yi gaggawar daukar matakin kashe gobarar.

Tsohon shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA), Dr. Mike Ogirima, wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce tayar ce ta faru ne bayan tashinta a filin jirgin saman Yola.

Sai dai jirgin ya yi hatsari ne a Abuja tare da jami’an bayar da agajin gaggawa don kashe gobarar kafin saukar fasinjojin a kan titin jirgin.

Ogirima ya ce, “Mun gode wa Allah.

Har yanzu muna kan titin jirgi kuma matukin jirgi ya tabbatar mana.

Ya kira stairs, yanzu haka muna sauka daga titin jirgin domin a kwashe mu zuwa ginin filin jirgin da ke zauren saukar baki.

“Mun yi wa Allah godiya saboda mun shaida yadda aka fiddo taya daga filin jirgin sama na Yola kuma mun shiga taron addu’a.

An sauke fasinjojin lafiya daga titin jirgin yayin da aka rufe titin na wani dan lokaci har sai an kwashe jirgin.

Wani jami’in kamfanin jirgin da ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin ya ce fasinjojin sun sauka lafiya.

Ya nuna godiya ga Allah da ya ba dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin lafiya lafiya.

Ya ce kamfanin jirgin zai sanar da hukumomin da suka dace a hukumance don gudanar da bincike kan lamarin.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *