Da Ɗumi Ɗuminsa! Shugaba Tinubu sake sabbin nade-naden mukamai

FB IMG 1696883339680

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sake amincewa da nada wasu mutane 6 a matsayin wadanda zasu Shugabanci hukumomin dake karkashin ma’aikatan sadarwa, kirkira da cigaban tattalin arzikin ta amfani da fasahar zamani.

Alfijir Labarai ta rawaito Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu.

Ga sunayen wadanda aka nada din ma’aikatun da aka tura su

(1) EVC / CEO, Nigerian Communications Commission (NCC) — Aminu Maida

(2) MD / CEO, Nigerian Communications Satellite Limited (NIGCOMSAT) — Nkechi Egerton-Idehen

(3) DG / CEO, National Information Technology Development Agency (NITDA) — Kashifu Inuwa Abdullahi

(4) National Commissioner / CEO, Nigeria Data Protection Commission (NDPC) — Dr. Vincent Olatunji

(5) Postmaster General / CEO, Nigerian Postal Service (NIPOST) — Tola Odeyemi

Sanarwar tace a kokarin Shugaban na Kara inganta ɓangaren fasahar zamani a Nigeria.

Ya kuma amince da nadin Idris Alubankudi a matsayin mai baiwa Shugaban kasa shawara na musamman a ɓangaren bunkasa tattalin arzikin ta amfani da fasahar zamani.

Sanarwar ta ce nadin nasu zai fara aiki ne nan take.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *