Ƴan Sandan Sun Kama Wadanda ake Zargi Da Kashe Ɗan Jarida

Screenshot 20221203 105846 com.facebook.katana edit 16220257093876

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe wakilin VON, Hamisu Dan Jibgan tare da wadanda ake zargin sun sayi kadarorin da aka kwashe bayan sun kashe marigayin.

Alfijir Labarai ta rawaito wadanda ake zargin a cewar ƴan sandan, su ne Mansur Haruna wanda ya kasance dan uwan marigayin ne da abokinsa Ibrahim Nababa da kuma wanda ya sayi dukiyar marigayin da aka sace, kuma dukkansu sun amsa laifin kashe.

Yayin holin wadanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Shehu Dalijan, ya ce da muka samu rahoton kashe dan jaridan, Hamisu Dan Jibga ƴan sanda sun dauki matakin damƙe wadanda ake zargin.

CP, ya ce wanda ake zargin na farko, Mansur Haruna, wanda ya kasance kanin dan uwa ne ga marigayin, ya bayyana wa yadda suka yi ta fama da marigayin a lokacin da suke son sace shi, da kuma duk abin da ya faru da ya kai ga yanke hukuncin karshe na kashe shi.

A wata hira da Mansur Haruna, ya bayyana cewa kawunsa, Ɗan Jibga ne ya kore shi daga gidansa saboda ya lura da yana sata, inda ya kara da cewa, “Kafin ya kore ni daga gidansa, sau biyu ina neman ya tsaya min na shiga aikin soja ko ɗan sanda, amma duk ya ki saboda mugun hali na”

Rundunar ‘yan sandan sun ce suna kokarin kammala bincike don mika su kotu tare da hukunta su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *