Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamnan Kano ya dakatar da Manajan Daraktan KASCO

Daga Abdu Ado K/Naisa

Gwamnan ya Bada Umurnin Binciken Gaggawa yayin da ya nanata alkawarin rashin amincewa da cin hanci da rashawa

Alfijir Labarai ta rawaito a ci gaba da kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Aikin Gona na Kano (KASCO) Dakta Tukur Dayyabu Minjibir.

Gwamnan ya bayar da umarnin dakatarwar ne a ranar Laraba 12 ga Satumba, 2023 wanda sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya sakawa hannu.

An dakatar da Manajan Darakta bisa zargin hannu a sayar da hatsin da bai dace ba na Gwamnatin Jihar Kano.

An umurci Dakta Dayyabu da ya mika al’amuran kamfanin ga babban jami’i nan take har sai an kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *