Cikakken Bayani kan gobarar da ta tashi a makarantar Northwest a kano

IMG 20250403 WA0567

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ƙonewar wasu ofisoshi a jami’ar North West da ke jihar Kano.

An dai ga wani faifan bidiyo yana kara-kaina a kafofin sadarwa, wanda yake nuna wuta tana tashi a benen mai hawa tara.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, SFS Kabiru Isah Jafar ya fitar, ya ce sun samu kiran kar-ta-kwana ne daga wani mai suna Mannir Abdullahi, wanda ya bayyana musu labarin gobarar.

“Jami’anmu sun isa wurin, wanda bene ne mai hawa tara. Wasu ofisoshi ne da wasu sassa na benen suka kama da wuta, amma babu wanda ya rasa rai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sun samu nasarar ciro kayayyakin dubban kuɗi a ofisoshin

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *