CBN Zai Kulle Miliyoyin Asusun Al’umma Daga Bankunan Kasa


Alfijr ta rawaito Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana shirin sa na dakatar da miliyoyin asusun bankunan mutane daga bankunan kasuwanci wadan da ba ayi rajista da BVN ba a dukkan fadin kasar Najeriya.

Daraktan kula da hadurra na babban bankin Najeriya Blaise Ijebor ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 6 ga watan Afrilu, ya kuma bayyana cewa burinsu shine domin su rage aukuwar hadurra da kuma zamba ko kuma damfara a Najeriya.

Da yake jawabi, darakta Ijebor ya ce lambar BVN wata alama ce ta musamman da ke daukar bayanan Kwastomomi, kuma ana amfani da ita domin a tantance sunayen su da kuma hana zamba.

Ya kara da cewa hukumar kula da harkokin kudi na shirin fara wannan aikin nan ba da jimawa ba, sai dai suna jiran CBN ya saka musu lokaci domin su fara aikin.

A ranar 2 ga watan Afrilu ne hukumar bincike ta NIBSS ta gudanar da wani bincike inda ta gano cewa akwai asusun banki miliyan 57.01 wanda ba ayi rajista da BVN ba a cikin jimillar asusun banki 191.4 da ke Najeriya.

Wannan ne ya sa babban bankin na CBN ya dauki aniyar kulle sauran miliyoyin asusan bankuna da ba ayi rajista da BVN ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “CBN Zai Kulle Miliyoyin Asusun Al’umma Daga Bankunan Kasa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *